Laraba 26 Agusta 2026 - 20:35
An Gano Tare da Tattara Taken Bincike 60,000 Kan Annabi Muhammad (SAWA), Za a Kaddamar da Kundin Juzu’i 12 a Taron Haɗin Kan Musulmi

Hauza/ A wani taron manema labarai da aka gudanar domin gabatar da “Kundin Batutuwan Bincike na Ilimomi da Ma’arifar Annabi Muhammad (SAWA)”, an bayyana cewa bayan kimanin shekaru 10 na bincike, tantancewa da tace bayanai, an gano tare da tsara batutuwa da maƙalolin bincike 60,000 da suka shafi halayya, rayuwa da koyarwar Annabi Muhammad (SAWA), waɗanda aka rarraba su zuwa fannoni 28 na ilimi.

A cewar rahoton Kamfanin Dillancin Labaran Hauza, an shirya wannan aiki cikin juzu’i 12, kuma ana shirin kaddamar da shi a birnin Qum yayin Taron Haɗin Kan Musulmi karo na 40.

Jami’an Makarantun Ilimin Addinin Musulunci (Hauza) sun jaddada cewa bincike kan Annabi Muhammad (SAWA) bai kamata ya takaita ga karatun littattafai kawai ba, a maimakon haka ya kamata ya dace da buƙatu da tambayoyin ɗan Adam a wannan zamani, musamman a fannoni kamar ɗabi’a (akhlaƙ), iyali, adalci, hankali, ilimin ɗan Adam da wayewar kai.

Bisa bayanan da aka gabatar, a matakin farko an tattara kusan batutuwa 70,000 na bincike, sannan bayan an gudanar da bincike, aka cire batutuwa masu maimaituwa tare da rarraba su bisa fannoni daban-daban na ilimi, sai aka samu batutuwa 60,000 da suka zama na ƙarshe a cikin wannan kundi.

Mai gudanar da wannan shiri ya kuma bayyana cewa kundin yana da tsari na wayewar kai da na ƙasa da ƙasa, inda ya ce batutuwan da aka tattara za su iya zama wata hanya ta bunƙasa binciken ilimi kan Annabi Muhammad (SAWA) a ƙasashen Musulmi daban-daban, tare da ƙarfafa haɗin kan masana a duniyar Musulmi.

Daga cikin batutuwan da aka tanada akwai nazarin dangantakar fahimtar ɗan Adam ta tsarin zamani na duniya da kuma fahimtar ɗan Adam da ɗabi’u bisa koyarwar Annabi (SAWA), da kuma nazarin tasirin ma’arifar Annabi Muhammad kan ginshiƙan iyali a zamanin Daular Usmaniyya da kuma al’ummar Turkiyya ta yau.

Jami’an makarantun Hauza sun bayyana fatan cewa wannan aiki zai taimaka wajen faɗaɗa binciken ilimi da aikace-aikace kan Annabi Muhammad (SAWA), samar da sabbin ra’ayoyin ilimi, da kuma gabatar da fa’idodin koyarwar Annabi ga al’ummar duniya.

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha